eMagazine Media Channel Featured MALAMAN MAIKALWA PRIMARY SUN GYARA RIJIYAR BOREHOLE, SADAKATU JARIYA
Featured

MALAMAN MAIKALWA PRIMARY SUN GYARA RIJIYAR BOREHOLE, SADAKATU JARIYA

1771251493072386 1

1771251493072386 1

MALAMAN MAIKALWA PRIMARY SUN GYARA RIJIYAR BOREHOLE, SADAKATU JARIYA

Malaman Makarantar Firamare na makarantar Maikalwa sun hada kudi domin gyaran borehole da ta lalace  mallakin makarantar, domin magance matsalar rashin ruwa da dalibai da malamai ke fuskanta.

Shugaban makarantar, Malam Ibrahim Ahmad, ya bayyana cewa wannan mataki da malamai suka dauka na gyaran rijiyar burtsatse, wani abin a yaba ne, domin ya nuna hadin kai da kishin ci gaban makarantar.

Malam Ibrahim Ahmad ya kara da cewa malamai sun bayyana cewa gudunmawar da suka bayar wajen gyaran borehole din suna kallonta a matsayin Sadaqatul Jariya, wadda za ta ci gaba da amfanar makarantar, dalibai da al’umma baki daya.

Ya ce gyaran borehole din zai taimaka matuka wajen samar da tsafta da saukaka harkokin koyarwa da koyo, tare da inganta walwalar dalibai a makarantar.

A karshe, shugaban makarantar ya yabawa malamai bisa wannan kokari, tare da yin kira ga sauran masu ruwa da tsaki da su kara bayar da gudunmawa domin inganta ci gaban makarantar.

Khadija Ahmed Musa

16/2/2026

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version