eMagazine Media Channel Education HUKUMAR KULA DA MANYAN MAKARANTUN SAKANDIRE TA JAHAR KANO (KSSSSMB) TA JADDADA ƘUDURINTA NA GANIN AN INGANTA TSARIN JARRABAWA A DUK MAKARANTUN SAKANDIRE NA FAƊIN JAHAR KANO.
Education Featured

HUKUMAR KULA DA MANYAN MAKARANTUN SAKANDIRE TA JAHAR KANO (KSSSSMB) TA JADDADA ƘUDURINTA NA GANIN AN INGANTA TSARIN JARRABAWA A DUK MAKARANTUN SAKANDIRE NA FAƊIN JAHAR KANO.

1764933048125

HUKUMAR KULA DA MANYAN MAKARANTUN SAKANDIRE TA JAHAR KANO (KSSSSMB) TA JADDADA ƘUDURINTA NA GANIN AN INGANTA TSARIN JARRABAWA A DUK MAKARANTUN SAKANDIRE NA FAƊIN JAHAR KANO.

1764933048125
DALIBAN DA SU KE RUBUTA JARRABAR SSQE.

Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Makarantun Sakandare na Jihar Kano, Alhaji Rabiu Sale Gwarzo, ya tabbatar da cewa hukumar na da cikakken Ƙudiri na tabbatar da bin ƙa’idoji da tsauraran matakai wajen gudanar da jarrabawa a dukkan makarantun sakandire a faɗin jahar Kano.

Wannan jawabi ya biyo bayan fara gudanar da Jarrabawar tantancewa ta ƙarshe(QUALIFYING EXAMINATION), inda kwamitin sa ido daga hukumar, ƙarƙashin jagorancin Daraktar Sa-ido da Kimantawa, suka kai ziyara zuwa makarantu domin duba yadda ake gudanar da jarrabawar.

An wakilci Sakataren Zartarwa da Daraktar Sa-ido da Kimantawa, Hajiya Halima Musa, wadda ta jagoranci tawagar, inda ta bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da kasancewa mai gaskiya, ladabi da kuma kishin tabbatar da sahihancin sakamakon jarrabawa. Daraktan ta ce, “tsauraran matakan sa-ido su ne ginshikin adalci da gaskiya a cikin jarrabawa.”

Sakataren Zartarwa ya yaba da haɗin kai da jajircewar shugabannin makarantu, malamai, masu sa-ido da dalibai wajen bin doka da oda, tare da bukatar su ci gaba da bin ka’idojin rubuta jarrabawa yadda ya kamata. Haka kuma, ya yaba wa gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf bisa irin matakan da take ɗauka wajen inganta harkar ilimi a fadin jahar Kano.

Tawagar sa-idon ta kunshi manyan jami’an sa-ido da aka tura zuwa makarantu daban-daban a fadin jihar. Daga cikin makarantun da aka ziyarta akwai

1- GGSS Giginyu,

2- GGSS Kundila, da

3- GGSS Kabo, da sauran makarantun da ke cikin birni da karkara.

A baya, yayin buɗe wannan aikin sa-ido, Daraktar Sa-ido da Kimantawa ta nuna godiya bisa irin kokarin da Sakataren Zartarwa ke yi wajen tabbatar da inganci da daidaito a tsarin gudanar da jarrabawa a makarantun sakandare na jihar.

Usman Datti Abdullahi

Daraktan Wayar da Kai da Jama’a

KSSSSMB

4/12/2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version