Press Release
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta Gudanar da Bita Kan Kariya Daga Gobara:

Daga: Usman Dau/Alhassan Hassan:
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta gudanar da bita kan hanyoyin kare kai da magance afkuwar gobara a gidaje, wuraren aiki da kasuwanni.
A jawabin sa na maraba, Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano (SUBEB), Malam Yusuf Kabir, ya bayyana cewa ma’aikatan hukumar sa, a shirye suke su karɓi duk wasu shawarwari da za su taimaka wajen hana faruwar gobara.
Shugaban, wanda ya samu wakilcin Kwamishina na Ɗaya na Hukumar, Hon. Wada Ibrahim Daho, ya bayyana cewa bitar za ta taimaka matuƙa wajen wayar da kan ma’aikata kan hanyoyin kare kansu da muhallinsu daga afkuwar gobara. Ya ƙara da cewa wannan bita ta zo a daidai lokacin da sanyi ke ƙara tunkarowa, wanda yakan haifar da yawaitar gobara a wasu lokuta.
Hon. Wada ya yi kira ga ma’aikata da su yi amfani da shawarwarin da za a ba su domin kauce wa afkuwar gobara.
A nasa jawabin, Jami’in Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, PFS Jamilu Abdullahi, ya bayyana cewa manufar bitar ita ce koyar da hanyoyin magance da kuma kare afkuwar gobara a ma’aikatu, gidaje da kasuwanni.
PFS Abdullahi ya ƙara da cewa, maimakon yawaitar samun kiran gaggawa daga al’umma, Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta bayar da umarnin gudanar da irin wannan bita ga ma’aikatan jihar domin kare kansu da muhallinsu daga gobara.
Bitar ta wuni guda da aka gabatar ta ƙunshi koyar da abubuwan da ke haddasa gobara da kuma hanyoyin kare kai idan gobara ta afku. Daga cikin abubuwan da aka bayyana na haddasa gobara akwai sakaci da rashin kulawa, amfani da wayar salula yayin girki da lodin wutar lantarki fiye da ƙima da rashin kashe lantarki lokacin bacci, da rashin tsaftar muhalli, da sauransu.
Taron bitar wayar da kan ya sami halartar daukacin daraktoci da ma’aikatan hukumar.
Corporate Communications Department,
SUBEB Kano.