eMagazine Media Channel Education HUKUMAR ILIMIN BAIƊAYA (SUBEB) TA JAHAR KANO TARE DA HADIN GUIWA DA KUNGIYAR NUT DA PLANE SUN FARA BAWA SABBIN MALAMAN MAKARANTA 4,315 HORO NA MUSAMMAN AKAN AIKIN KOYARWA. 
Education

HUKUMAR ILIMIN BAIƊAYA (SUBEB) TA JAHAR KANO TARE DA HADIN GUIWA DA KUNGIYAR NUT DA PLANE SUN FARA BAWA SABBIN MALAMAN MAKARANTA 4,315 HORO NA MUSAMMAN AKAN AIKIN KOYARWA. 

aiposter 2026 01 05 092429

HUKUMAR ILIMIN BAIƊAYA (SUBEB) TA JAHAR KANO TARE DA HADIN GUIWA DA KUNGIYAR NUT DA PLANE SUN FARA BAWA SABBIN MALAMAN MAKARANTA 4,315 HORO NA MUSAMMAN AKAN AIKIN KOYARWA.

Hukumar ilimin baiɗaya ta jahar Kano tare da haɗin guiwa da kungiyar malaman makaranta na jahar Kano da kuma kungiyar PLANE sun fara ba wa sabbin malaman makaranta waɗanda gwamnatin jahar Kano ta ɗauka aiki a shekarar 2025 domin kara musu sani a fannin dabarun koyo da koyarwa. Horon an fara gabatar da shi ne a cibiyoyin da aka samar a fadin jahar Kano a inda aka fara gabatar da horon a Makarantar Dukawuya Girls Science Project dake karamar hukumar Gwale. Zagayen da muka yi a wannan rana ta Litinin 5/1/2025 , mun je santar Dukawuya Girls Science a inda ake ba wa malaman da suka futo daga karamar hukumar Gwale da Madobi da kuma Kumbotso. Sai kuma santar Takai wadda ta ƙunshi malaman da suka futo daga karamar hukumar Takai da Albasu da kuma Sumaila . Sai sauran santocin da suka haɗa da Gaya da Dawakin Kudu da Karaye da sauransu.

aiposter 2026 01 05 054948

Wannan horo ya samu halartar mafiyawan malaman da aka gayyata.

Malaman sun yaba da wannan horo da ake basu tare da yin godiya ga gwamnatin jahar Kano bisa jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf da shugaban hukumar ilimin baiɗaya Alhaji Yusuf Kabir. Haka zalika malaman sun isar da sakon godiya da yabo na musamman ga shugaban ƙungiyar malaman makaranta na jahar Kano Comrade Baffa Ibrahim Garko bisa taimaka musu da ya yi wajan ɗaukansu aiki na dundundun.

Baba Comrade, E-Magazine & Khadija Ahmed Musa Kumbotso

5/1/2026

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version