eMagazine Media Channel Politics Hujja Ba Karya Ba: Kallon Kalubalen Dan Bilki Comanda da Kuma Zahirin Ayyukan Gwamna Abba Kabir Yusuf
Politics

Hujja Ba Karya Ba: Kallon Kalubalen Dan Bilki Comanda da Kuma Zahirin Ayyukan Gwamna Abba Kabir Yusuf

IMG 20260228 WA0006

IMG 20260228 WA0006

Hujja Ba Karya Ba: Kallon Kalubalen Dan Bilki Comanda da Kuma Zahirin Ayyukan Gwamna Abba Kabir Yusuf

Daga: Mohammed Babagana Abubakar

Kano State Coordinator, Unifier Project

aunodigitalabuba@gmail.com

11 April, 2026

 

A tsarin dimokuradiyya, adawa abu ne mai kyau domin tana sa gwamnati ta kara kaimi, amma idan adawa ta koma ta surutai ba tare da hujja ba, ko kuma ta zama kokarin shafa wa gaskiya kashin kaza, to lallai ta fita daga layin gina kasa. A kwanakin nan, muna jin kalaman kalubale daga bakin Dan Bilki Comanda, wadanda idan aka duba su da idon basira da kuma zahirin abin da ke kasa a Jihar Kano, za a ga cewa kalaman sun yi hannun riga da gaskiya.

 

Gwamnati a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ba ta gina aikinta akan boye boye ko tallan karya ba. Maimakon hakan, ta zabi ta bar ayyukanta su yi wa kansu magana. Daga lungu da sako na Jihar Kano, akwai alamun ci gaba da ayyukan raya kasa wadanda ba bukatar wani ya gaya maka kafin ka gansu.

 

Daya daga cikin manyan kalubalen da masu adawa irin su Dan Bilki ke kaucewa magana akai shi ne juyin juya halin da aka samu a fannin ilimi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fahimci cewa ilimi shi ne ginshikin cigaba:

 

An biya wa dubun dubatar daliban jihar kudaden jarrabawar NECO da WAEC, wanda hakan ya rage wa iyaye radadin talauci.

 

Shirin tura dalibai 1,001 zuwa kasashen ketare don karo ilimi babban bargo ne da ya rufe kowane irin surutu na adawa.

 

Gyaran makarantun firamare da sakandare a fadin jihar, ciki har da samar da kujeru da tebura wadanda a baya aka bar dalibanmu suna zama a kasa.

 

A yayin da masu adawa ke kokarin boye gaskiya, al’ummar Kano suna shaida canje canje a asibitocinmu ta hanyar shirin Lafiya Dole. Samar da na’urorin kiwon lafiya na zamani da kuma inganta asibitocin karkara ya rage wa marasa karfi radadi. Wadannan ayyuka ne da talaka ke amfana da su kai tsaye, ba wai tatsuniyoyin rediyo ba.

 

A zahiri, kowa ya sani cewa tituna da gadoji su ne alamun ci gaban birni. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da hankali wajen.

 

Gina manyan gadoji (Flyovers) a wurare masu cunkoso don saukaka zirga zirga.

 

Maido da fitulun kan hanya (streetlights) wadanda ke taimakawa wajen tsaro da kuma kyawun birninmu na Kano.

 

Farfado da madatsun ruwa domin tabbatar da cewa ruwa ya isa kowane gida a cikin birnin Kano da kewayenta.

 

Maimakon Dan Bilki Comanda ya rika amfani da kalamai na neman suna ko farfaganda, ya kamata ya fito fili ya gaya wa duniya wanne ne daga cikin wadannan ayyukan ba a yi su ba? Gaskiya daya ce kuma ba ta neman riga.

 

A matsayinmu na masu ruwa da tsaki a karkashin inuwar Unifier Project, muna kira ga al’umma da su zama masu tantance labarai. Jihar Kano tana kan tafarki na gari, kuma za mu ci gaba da tsayawa kan gaskiya domin kare muradun al’ummar Jihar Kano.

 

Allah ya ba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ikon ci gaba da hidimta wa al’umma.

 

Mohammed Babagana Abubakar

Kano State Coordinator, Unifier Project

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version