eMagazine Media Channel News Gwamnatin Kano ta fara Tattaunawa da Masu Gabatar da Shirye-Shiryen Siyasa a kafafan yaɗa labarai don dakile Maganganun batanci da Ƙalubalen Tsaro a jahar Kano.
News

Gwamnatin Kano ta fara Tattaunawa da Masu Gabatar da Shirye-Shiryen Siyasa a kafafan yaɗa labarai don dakile Maganganun batanci da Ƙalubalen Tsaro a jahar Kano.

images

 Gwamnatin Kano ta fara Tattaunawa da Masu Gabatar da Shirye-Shiryen Siyasa a kafafan yaɗa labarai don dakile Maganganun batanci da Ƙalubalen Tsaro a jahar Kano.

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudurinta na yin aiki kafada da kafada da masu gabatar da shirye-shiryen siyasa a gidajen rediyo domin inganta tattaunawa mai ma’ana a bainar jama’a da kuma hana amfani da kafafen watsa labarai wajen yada bayanan ƙarya, musamman game da lamuran tsaro.

Wannan tabbaci ya fito ne a wani taro da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jagoranta tare da shugabannin ƙungiyar masu gabatar da shirye-shiryen siyasa a gidajen rediyo na Kano, wanda aka gudanar a dakin taro na ma’aikatar yaɗa labarai.

Da yake jawabi a taron, Comrade Waiya ya bayyana cewa wannan haɗin guiwa ya zama dole duba da wasu matsalolin tsaro da ke faruwa a wasu kananan hukumomi da ke iyaka da Jihar Katsina, wanda ya haifar da karuwar damuwa da muhawara a kafafen watsa labarai.

Kwamishinan ya jaddada cewa duk da muhimmancin shirye-shiryen siyasa wajen haɓaka dimokuraɗiyya, masu gabatar da shirye-shiryen na da alhakin yin taka-tsantsan da ƙwarewa wajen mu’amala da batutuwan da suka shafi tsaro.

Ya bukaci mambobin ƙungiyar da su guji bayar da dama ga ‘yansiyasa da masu ruwa da tsaki su tattauna batutuwan tsaro a cikin shirye-shiryen siyasa, yana mai cewa irin waɗannan batutuwa ya kamata a bar su ga shirye-shiryen labarai da namusamman da aka tsara domin bayar da sahihan bayanai ga hukumomi.

A cewarsa, tattaunawar  ba ta da  harkokin tsaro daga bakin ‘yan siyasa na haifar da jita-jita, yada ƙarya da tayar da hankalin jama’a ba tare da buƙata ba. Ya gargadin  cewa nuna Kano a matsayin wuri mai  matsalolin tsaro na iya rage kwarin guiwar jama’a da yin tasiri mara kyau ga zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin jihar.

Comrade Waiya ya sake jaddada cewa, Gwamnatin Jihar Kano na da cikakken iko da al’amuran tsaro a jihar, tare da haɗin guiwa da hukumomin tsaro domin magance duk wata barazana da ka iya tasowa. Ya yi kira ga masu gabatar da shirye-shiryen siyasa a gidajen rediyo da su mara wa ƙoƙarin gwamnati baya ta hanyar tabbatar da cewa tattaunawa a shirye-shiryensu na gaskiya ne kuma akan daidai.  Kuma tattaunawar ta zama wacce za ta haɓaka zaman lafiya da ci gaba ne . Amma tada hankalin jama’a ba.

Ya yaba da haɗin kan mambobin ƙungiyar tare da gwamnatin jihar, inda ya buƙace su da su ci gaba da kiyaye ƙa’idojin aikin jarida, ƙwarewa, da kuma amfani da aikinsu wajen bauta wa jama’a cikin amana.

A nasa martanin, Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Masu Gabatar da Shirye-Shiryen Siyasa na Gidajen Rediyo a Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Wali, ya tabbatar da kudurin mambobinsu na bin doka da ka’idoji wajen gabatar da shirye-shirye masu inganci.

IMG 20251222 WA0026 640x359

Ya tabbatar wa kwamishinan cewa za su ƙara sa ido a tattaunawar siyasa da ake yi a dandamalinsu, tare da dakile yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba, musamman wadanda suka shafi harkokin tsaro.

Baba Comrade, E-Magazine

Daga Hukumar yada labarai na jahar Kano.

22/12/2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version