eMagazine Media Channel News GWAMNATIN JAHAR KANO TA ƘARYATA ZARGIN DA AKE MATA NA ƘARYA AKAN KASAFIN KUDI….
News Politics

GWAMNATIN JAHAR KANO TA ƘARYATA ZARGIN DA AKE MATA NA ƘARYA AKAN KASAFIN KUDI….

Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano Ta Bayyana Ci Gaban Da Aka Samu, Ta Karyata Zarge-Zargen Ƙarya Kan Kasafin Kuɗi.

Gwamnatin Jihar Kano ta karyata ikirarin da Babban Mai Taimakawa Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa na baya-bayan nan, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi — wanda kuma ya kasance Kwamishinan Yaɗa Labarai a lokacin mulkinsa — dangane da zargin raunin aiwatar da kasafin kuɗi a bangarori daban-daban na rahoton kasafin kwata na uku na shekarar 2025.

Kwamishinan Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi na jihar Kano, Alhaji Musa Sulaiman Shanono, ya yi ƙarin haske akan wannan zargi a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba a ma’aikatar. Ya bayyana ce wa, fassarar rahoton kasafin da wata kafar yada labarai ta yanar gizo a Kano ta wallafa ya kasance mai ɗauke da ɓangaranci da rudani.

Shanono ya bayyana ce wa, rahoton da ke cewa bangarorin kamar Ruwa, Lafiya da Ilimi sun samu ƙasa da kashi 40 cikin 100 wajen aiwatar da manyan ayyuka daga Janairu zuwa Satumba 2025, bai yi kwatancen sakamakon da na gwamnatin da ta gabata ba. Ya jaddada ce wa , bincike a rahoton kwata na uku na shekarar 2022 — wanda ke a fili a shafin kasafin kuɗin jihar — ya nuna ce wa waɗannan bangarori sun fi yin rauni a ƙarƙashin gwamnatin baya.

Ya bayyana ce wa kuma a shekarar 2022, Ma’aikatar Lafiya duk da samun kason kasafin kuɗi na Naira biliyan 18.8, ta aiwatar da Naira miliyan 468.6 kawai, wanda ke wakiltar kashi 2.5 cikin 100 kacal. Haka kuma, ya ƙara da cewa Ma’aikatar Ilimin Gaba da Sakandire bata aiwatar da komai ba a fannin manyan ayyuka a wannan lokaci.

A gefe guda, rahoton kwata na uku na shekarar 2025 ya nuna ci gaba a ƙarƙashin gwamnatin yanzu. Bangaren lafiya ya samu kashi 12 cikin 100, Ilimi ya cimma kashi 32.2 cikin 100, yayin da Ruwa ya samu kashi 13.4 cikin 100 — alkaluman da ya bayyana a matsayin alamu na ci gaba ba koma baya ba.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta  assasa wutar lantarki da samar da ruwa. Ya bayyana aikin farfaɗo da Tiga Hydropower Project da kuma bashin da aka tarar a Challawa Power Plant wanda ya haɗa da bashi na dala miliyan ɗaya daga ƙetare da kuma bashin cikin gida na Naira biliyan 7. Ya ce a baya layin rarraba wutar jihar Kano yana ƙarewa ne a Tamburawa ba tare da isassun masu amfani ba, amma yanzu an shimfiɗa shi zuwa Hadejia Road don ƙara ƙarfin rarrabawa.

Game da samar da ruwa, Shanono ya bayyana cewa gwamnati ta sayo famfunan ruwa na zamani guda 10 — shida don Challawa da huɗu don Tamburawa — don ƙara samar da ruwa a cikin birni. Haka kuma, ya ambato cigaban da ake samu wajen horar da injiniyoyi da ma’aikatan fasaha na Water Board.

Ya ƙara da cewa ana samun irin wannan cigaba a fannin ilimi ta hanyar sabbin jarin gine-gine, ci gaban malamai da ingantattun kayan koyo da koyarwa.

Don tabbatar da jajircewar gwamnati wajen gaskiya da ɗawainiya, Kwamishinan ya bayyana cewa Jihar Kano na ci gaba da fitar da rahotannin kwata-kwata na aiwatar da kasafi a cikin lokacin da ya dace, domin bai wa jama’a cikakken damar samun bayanan kuɗaɗe.

Ya tabbatar wa da al’umma cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf na ci gaba da mayar da hankali kan sake gina muhimman ababen more rayuwa, inganta ayyukan gwamnati da bunƙasa rayuwar al’umma baki ɗaya.

Baba Comrade, E-Magazine

05/12/2025

images (7)
Alh. Musa Sulaiman Shanono , Kwamishinan Kasafi na jahar Kano.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version