eMagazine Media Channel LABARAI EFCC Ta Janye Ƙarar da Ta Shigar da Maryam Shehu da Wanda Ake Zargi Tare da Ita
LABARAI

EFCC Ta Janye Ƙarar da Ta Shigar da Maryam Shehu da Wanda Ake Zargi Tare da Ita

IMG 20260821 WA0005

IMG 20260821 WA0005

EFCC Ta Janye Ƙarar da Ta Shigar da Maryam Shehu da Wanda Ake Zargi Tare da Ita

Hukumar Yaƙi da cin hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta janye ƙarar da ta shigar kan mai wallafa labarai ta yanar gizo daga Kano, Maryam Isah Shehu, da kuma Abubakar Shuraim Abdulhamad, bayan shiga tsakani da Shugaban Hukumar, Mista Ola Olukoyede.

An gurfanar da matasan ’yan Najeriya biyu a ranar Alhamis, 20 ga Agusta, 2026, a gaban maishari’a Joyce Abdulmalik ta Kotun Ƙoli ta Tarayya da ke Abuja, bisa zargin aikata laifukan yanar gizo da kuma yaɗa bayanan da EFCC ta bayyana a matsayin masu ɓarna ko cutarwa ga hukumar.

EFCC ta bayyana cewa an yanke shawarar janye ƙarar ne bayan Olukoyede ya yi la’akari da roƙo mai ƙarfi da kuma neman afuwa daga mahaifin Maryam Shehu, tare da roƙon wasu ’yan Najeriya masu kishin ƙasa da suka nemi a yi wa waɗanda ake zargin sassauci.

A cewar hukumar, Olukoyede ya bayar da umarnin cikin tausayi cewa a janye ƙarar da ake yi wa waɗanda ake zargin, duk da cewa EFCC ta tsaya kan matsayinta cewa abin da ake zargin sun aikata ya kasance laifi ne ƙarƙashin Dokar Laifukan Yanar Gizo ta Cybercrimes (Prohibition, Prevention, Etc.) Act, 2015, wadda aka yi wa gyara a shekarar 2024.

EFCC ta ce an gurfanar da waɗanda ake zargin ne dangane da abin da ta kira “cybercafe stalking”, wanda ta ce ya saɓa wa Sashe na 24(2)(c) na Dokar Cybercrimes, kuma hukunci ya tanada a ƙarƙashin Sashe na 24(2)(c)(ii) na dokar.

Sai dai shugaban hukumar ya yi amfani da ikon da doka ta ba shi wajen dakatar da shari’ar, bayan ya karɓi roƙon a yi wa waɗanda ake zargin sassauci.

Wannan mataki ya kawo ƙarshen gurfanarwar da aka fara kan Shehu da Abdulhamad, sai dai ana buƙatar kammala matakan doka da suka dace domin janye ƙarar a gaban kotu.

Wannan ci gaba na da matuƙar muhimmanci musamman a batun Maryam Shehu, wadda rahotannin tsare ta suka jawo hankalin jama’a, tare da kiran magoya bayanta da masu kare haƙƙin bil’adama na a sake ta.

Tun da farko, Lauyan Kare Haƙƙin Bil’adama, Barrister Abba Hikima, ya nuna damuwa kan ci gaba da tsare Maryam, inda ya bukaci EFCC da ko dai ta gurfanar da ita a gaban kotun da ta dace idan tana da isassun hujjojin aikata laifi, ko kuma ta sake ta idan babu wani dalili na doka da zai sa a ci gaba da tsare ta.

Abba Hikima da wasu magoya baya, ciki har da Barrister Nuhu Dantani, sun kuma yi kira ga ƙungiyoyin da abin ya shafa da su shiga tsakani, suna mai cewa bai kamata bincike ya koma wata hanya ta hukunta mutum ba.

Wannan fafutuka ta jawo hankalin jama’a sosai, inda magoya bayan Maryam suka yi amfani da alamar #FreeMaryamShehu, suna neman a sake ta tare da ƙarin bayani da gaskiya game da dalilan da suka sa aka tsare ta.

Sabon matakin EFCC na janye ƙarar ya zama wani babban ci gaba a cikin wannan lamari.

Sai dai yayin da take bayyana dalilin matakin nata, hukumar ta jaddada cewa ba za ta amince da abin da ta kira hare-haren ganganci da ake kai wa martabarta ba.

Hukumar yaki da cin hancin ta yi gargadin cewa ba za ta ɗauki wasa ba kan suka ko wani hali da aka nufa da shi wajen lalata mutuncinta ta kowace kafar sadarwa ko dandali.

Duk da janye ƙarar, hukumar ta jaddada cewa bai kamata a fassara matakin nata a matsayin ta barin nauyin da doka ta ɗora mata ba.

Olukoyede ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa EFCC za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa ƙa’idodin da aka kafa ta a kansu, tare da fifita muradun ƙasar.

Matsayar hukumar na nuna cewa, duk da ta yi amfani da sassauci a wannan lamari sakamakon roƙon da aka yi a madadin waɗanda ake zargin, har yanzu tana da ƙudurin kare mutunci da martabar hukumar.

Janye ƙarar ya kuma zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara a tsakanin jama’a kan daidaita ikon hukumomin tabbatar da doka, ’yancin faɗar albarkacin baki da kuma haƙƙin ’yan ƙasa da ake bincike a kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version