eMagazine Media Channel Politics Dimbin Jama’ar Kano Sun Tarbi Gwamna Abba Yusuf, Mataimaki na musamman na miƙa godiya tare da kira da a ci gaba da Goyon Bayan Gwamna Abba 
Politics

Dimbin Jama’ar Kano Sun Tarbi Gwamna Abba Yusuf, Mataimaki na musamman na miƙa godiya tare da kira da a ci gaba da Goyon Bayan Gwamna Abba 

IMG 20260405 WA0022

IMG 20260405 WA0022

Dimbin Jama’ar Kano Sun Tarbi Gwamna Abba Yusuf, Mataimaki na musamman na miƙa godiya tare da kira da a ci gaba da Goyon Bayan Gwamna Abba

Mataimaki ga Gwamnan Jihar Kano, Hon. Umar Yushau Rurum, ya bayyana matuƙar godiyarsa ga miliyoyin al’ummar jihar Kano da suka fito taron  tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf a lokacin dawo warsa jahar Kano.

Da yake magana a madadin magoya bayan gwamnan, Rurum ya bayyana wannan gagarumin fitowar jama’a daga dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar a matsayin babbar shaida ta haɗin kai da kuma amincewar jama’a da jagorancin Gwamna Yusuf, wanda aka fi sani da “Abba Gida Gida.”

Ya kuma yaba da salon mulkin gwamnan wanda ya mayar da hankali kan jin daɗin jama’a, inda ya jaddada ƙudirin gwamnati wajen mutunta ɗan Adam, gudanar da shugabanci nagari, da kuma aiwatar da manyan ayyukan ci gaba a birane da karkara.

Rurum ya ƙara da kira ga al’ummar Jihar Kano da su ci gaba da bai wa gwamnan goyon baya, tare da roƙon su da su riƙa yi masa addu’a domin samun nasara da shiriya. Ya bayyana cewa, tabbas  Gwamna Yusuf zai samu ƙarin nasarori tare da sake samun damar ci gaba da mulki a wani wa’adi na gaba.

Hon. Rurum shi ne mai magana da yawun ƙungiyar masu goyon bayan gwamnan, kuma Mataimaki na Musamman kan wayar da kan jama’a.

Domin samun talla da sakonnin siyasa da sanarwa da wallafe-wallafen labarai, za ku iya kiranmu ta kan wannan lambar waya 08036614747

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version