Shugaban NUT na Kano ya taya Gwamna da malaman makaranta murnar Babbar Sallah; Ya jinjinawa gwamna Abba akan bawa ma’aikata ₦20,000
Shugaban Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT), reshen Jihar Kano, Kwamared Baffa Ibrahim Garko, ya mika sakon taya murnar Babbar Sallah ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, mambobin Majalisar Zartarwa ta Jiha, da daukacin al’ummar musulmai musamman malaman makaranta na jahar Kano.
Yayin da yake magana a madadin dukkanin mambobin Kwamitin Zartarwa na Jiha (SWEC), Kwamared Garko ya bayyana godiyarsa ga Gwamnatin Jihar Kano bisa biyan kudin kyautar Babbar Sallah ga ma’aikata, musamman malamai, inda ya bayyana wannan mataki a matsayin abu maikyau.
Shugaban, ya taya dukkan malamai na Jihar Kano murnar Babbar Sallah tare da addu’ar Allah Ya karɓi ibadunmu na wannan lokaci na ibadar sallah babba.
Kwamared Garko ya kuma yi addu’ar dorewar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban Jihar Kano da Najeriya baki daya.
Sa hannu:
Kwamared Baffa Ibrahim Garko
