Politics

WAIYA, LIMAMIN MANUFARMU KANO! – Sufyan

IMG 20260220 WA0005(1)
IMG 20260220 WA0005(1)

WAIYA, LIMAMIN MANUFARMU KANO!

– Sufyan Lawal Kabo

FASSARA DAGA BABA COMRADE

Hon (Amb) Ibrahim Abdullahi Waiya, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, ya fito karara a matsayin ɗaya daga cikin mambobin majalisar zartarwa na Gwamna Abba Kabir Yusuf da suka fi shahara, jajircewa, kuzari da iya magana – ba kawai a cikin gwamnati ba, har ma a faɗin Jihar Kano baki ɗaya. Wannan ya yi daidai da irin hasashen da da yawa daga cikinmu muka yi lokacin da aka naɗa shi shekaru biyu da suka gabata. Bisa la’akari da asalinsa, gogewarsa da kuma jajircewarsa wajen yi wa al’umma hidima, a fili yake cewa zai zo da wani salo na musamman a harkar mulki.

Sai dai abin da ya fi bambanta Waiya ba kawai ƙwarewarsa ba ce, har ma da irin amincewa da kusancin da yake da shi da Gwamnan Jihar. Yana daga cikin amintattun mutanen Mai Girma Gwamna, wanda ya fahimci manufofinsa sosai kuma yake bayyana su da cikakken haske, ƙwazo da aminci. Ƙwarewarsa wajen fassara manufofi, kare su da kuma gabatar da su cikin ƙarfi da gamsasshen bayani na nuna kyakkyawar alaƙar aiki wadda ta ginu bisa amincewa da mutunta juna. A hanyoyi da dama, ba kawai Kwamishina ba ne, har ma ginshiƙi ne mai ƙarfi wajen bunƙasa da kare martaba da alkiblar gwamnatin.

Da asalin gwagwarmayarsa, zurfin iliminsa da jajircewarsa ba tare da tsoro ba, Waiya ya kafa kansa a matsayin “Super Commissioner” – murya mai ƙarfi kuma ginshiƙin dabaru a cikin majalisar zartarwa. Yayin da manufar KANO FIRST (MANUFARMU KANO)ke ci gaba da bunƙasa, ba za a iya mantawa da rawar da yake takawa a matsayin ɗaya daga cikin jagororin da ke tafiyar da ita ba, yana tsayawa kafada da kafada da Gwamna wajen ƙarfafa hangen nesansa a kowane mataki.

Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ci gaba da tsare shi, Ya ba shi shiriya, Ya ƙara masa ƙarfi da basira, tare da ɗaga darajarsa zuwa matakai mafi girma a hidima ga al’umma. Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *