News

Commissioner Waiya ya ba wa shugaban OKA Mota

IMG 20260210 180553 903
IMG 20260210 180553 903

Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida na jahar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya ba wa shugaban kungiyar One Kano Agenda (OKA) dalleliyar mota kirar Honda.

Comrade Abdullahi Waiya ya ce, mun ba wa Ambassador Abbas Yakasai motar ne saboda sadaukar da lokutansa da jikinsa wajan hidimtawa jahar Kano. Waiya ya ƙara da cewa , Yakasai bashi da abun hawa a duk wannan Lokacin da ya sadaukar da rayuwarsa akan hidimtawa jahar Kano ta fuskoki da dama, waɗanda suka haɗa da harkar ba wa matasa ilimi , tabbatar da tsaro da kuma wayar da kan al’ummar jahar Kano musamman akan illar sha da fataucin muggan kwayoyi. Wanda hakan ne ya sa ya kafa kungiyar One Kano Agenda domin sanya muradun Jahar Kano a gaba.

IMG 20260210 180509 398

A nasa jawabin sakataren kungiyar OKA Munir Ibrahim(Publisher) ya mika sakon godiya ga Honourable Commissioner Waiya bisa wannan mota da ja ba wa jagoran OKA. Domin wannan abun da ya yi wa shugaban OKA ba shi kadai ya yi wa ba , domin abun ya shafi dukkanin membobin OKA da ma al’ummar jahar Kano baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *