Education

NUT:GWAMNA ABBA BA KA DA MATSALA DAGA MALAMAI MATUKAR KA DAIDAITA ALBASHI

IMG 20260127 WA0014
IMG 20260127 WA0014

NUT: GWAMNA ABBA BA KA DA MATSALA DAGA MALAMAI MATUKAR KA DAIDAITA ALBASHI NA MAFI KARANCIN ALBASHI NA 70,000

Ƙungiyar NUT ta ƙasa reshen Jahar Kano ta ce , matuƙar Gwamnan jahar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya daidaita matsalar albashin malaman makaranta daidai da tsarin minimum wage na 70,000 , to ko shakka babu malaman makaranta na jahar Kano za su taimaka masa 100% akan dukkannin bukatunsu.

Shugaban ƙungiyar malaman makaranta na jahar Kano Comrade Baffa Ibrahim Garko ya bayyana cewa, matukar maigirma Gwamnan jahar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya daidaita albashin malaman makaranta na Primary to ko shakka babu malaman za su yi farin ciki da hakan tare da nuna cikakken goyon baya ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf. Garko ya bayyana hakan ne a ranar Talata 27/1/2026 a wata hira da ya yi a wata kafar yada labarai a jahar Kano.

Garko ya kuma ce, kungiyar NUT ba za ta sake yadda ake cin zarafin malaman makaranta ba, ba da wani dalili na karya dokar aiki ba. Garko ya kuma ja kunnen malaman makaranta da su zage dantse wajan yin aiki tukuru bisa gaskiya da amana.

Garko ya ce kungiyar NUT ta fara wani yunkuri na koya wa malaman makaranta wasu sana’o’i na dogaro da Kai bayan sun yi ritaya (Rayuwa Bayan Ritaya). Domin yin hakan zai tai maka wa duk wanda ya gama aiki wajan samun kwanciyar hankali da nutsuwa.

Garko ya yi kira ga gwamnatin jahar Kano da ta fitar da tsarin ba wa school principals kuɗin Duty Post da kuma kuɗin Impressed domin gudanar da aikin makarantu yadda ya kamata. Saboda a halin da ake ciki yanzu shugabannin makarantu su ke ɗaukan nauyin wasu abubuwan na gudanar da makarantu da kudinsu, duk da dai gwamnati tana iya kokarinta wajan samar da kayayyakin aikin koyo da koyarwa da gyara makarantu da kuma yi wa malaman makaranta promotion. NUT tana yaba wa Gwamnan jahar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf wajan kula da harkar ilimi da kuma biyan albashi akan lokaci.

Garko ya yi kira ga malaman da su taya kungiyar da addu’a wajan samun nasarorin da ake bukata domin shawo kan duk wata matsala da ta shafi malaman makaranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *