Condolences

AOPSHON Ta Kai Ziyarar Ta’aziyya

IMG 20260121 143950 812
IMG 20260121 143950 812

AOPSHON Ta Kai Ziyarar Ta’aziyya

Ƙungiyar Shugabannin Makarantun Firamare ta Najeriya (AOPSHON), reshen Karamar Hukumar Gwale, ta kai ziyarar ta’aziyya ga wasu malamai da shugabannin makarantu da suka rasa iyayensu kwanan nan bisa jagorancin Sakatariyar ƙungiyar ta jahar Kano, Comrade Bilkisu T Abdulƙadir

IMG 20260121 142943 476

A ranar Alhamis, 21 ga Janairu 2026, reshen AOPSHON na Karamar Hukumar Gwale ya gudanar da zagayen kai ta’aziyya domin jajanta wa malaman da suka fuskanci rasuwa a cikin satin. Ƙungiyar ta ziyarci iyalan marigayi Baba Bashir, mahaifin Malama Aisha Baba Bashir (Mataimakiyar Shugabar Makaranta, MMG/Kaya SPS).

Haka nan kuma, ƙungiyar ta kai ziyarar ta’aziyya ga Malama Rabi Ibrahim, Shugabar Makarantar Ubaiyu bin Ka’abu Islamiyya Primary School, bisa rasuwar mahaifiyarta.

Sakatariyar AOPSHON ta Jihar Kano, Comrade Bilkisu T. Abdulqadir, ta isar da sakon ta’aziyyar ƙungiyar ga malaman a madadin shugabancin ƙungiyar, tare da yin addu’ar Allah Ya ji ƙanan mamatan Ya kuma gafarta musu.

Ta samu rakiyar wakilan reshen Karamar Hukumar Gwale, waɗanda suka haɗa da Malama Amina Ali Dambatta, Shugabar Makarantar Abubakar Nasoro Islamiyya Primary School, da kuma Malama Zahrau Abdullahi, Shugabar Makarantar Dansarkin Kura Islamiyya Primary School.

Allah Ya ji ƙanan mamatan da rahama.

Baba Comrade, E-magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *