Ƙalubalen da hare haren Amurka a Najeriya zasu haifar–Durumin Iya
Fitaccen masanin harkokin tsaro Detective Auwal Bala Durumin Iya, ya bayyana wasu daga cikin ƙalubalen da za’a iya fuskanta biyo bayan ƙaddamar da hare haren Amurka a yankin arewacin Najeriya.
Durumin Iya, yace babban kalubalen da za a fuskanta a hareharen shi ne duk lokacin da aka yi kuskure wajen kaiwa musulmai hari za a yiwa hakan wata irin fahimta sakamakon cewa wasu zasu ɗauki cewa mabiya addinin kirista ake yiwa aiki ba wai yan ta’adda ake farmaka ba.
Haka zalika, yace wannan hali da ake ciki na iya haifar da rikici tsakanin musulmi da kirista, musamman idan Amurka ta yi kuskuren kai hari ko kashe musulmi yan-ba-ruwana.
Idan har ana son zaman lafiya to dole ne a tabbatar ƴanta’adda Amurka ta ke kaiwa harehare ba wai fararen hula ba, inji Durumin Iya.
A wani cigaban, masanin sha’anin tsaron yace dole ne gwamnati ta ɗauki mataki kan masu yaɗa labaran ƙarya dangane da cewa ana yin kisan gilla ga mabiya addinin kirista a Najeriya, musamman masu haɗa hotunan ƙarya don janyo hankalin ƙasashen waje da tayar da rikici a cikin gida.
Durumin Iya, yace tabbas Amurka za ta taimaka wajen kakkaɓe ƴan ta’adda daga Najeriya, in har an yi hakan ta hanyar da ta dace, bisa hujjar sa cewa Amurka ba zata samu matsalar kaiwa yan ta’adda hari ba, kamar yadda jami’an tsaron Najeriya ke samun tangarda a yayin kai hari.
Haka zalika yace hakan zai taimaka wajen bankaɗo masu hannu a rura wutar ta’addanci a Najeriya , saboda Amurka tana da hanyoyi sahihai na samun bayanan sirri, yana mai cewa hakan zai sa a hukunta masu irin wannan hali, saboda ƙasar Amurika tana kashe kuɗaɗen ta sosai a sha’anin tsaro.
Idan za’a iya tunawa dai a daren Juma’a da ta gabata ne Amurka ta ƙaddamar da hare haren jirgi mara matuƙi zuwa wasu yankunan jihar Sokoto, inda tace an kai harin zuwa ga maboyar mayaƙan ISIS.
Sai dai wasu daga cikin al’ummar yankin da aka kai harin sun ce babu yan ta’adda a wajen kuma babu mutum ɗaya da harin ya kashe.
Shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar a daren Juma’a cewa shine ya jagoranci bayar da umurnin yadda harin ya kasance, sannan yace an samu nasarar kai harin kamar yadda aka tsara.
A nata martani gwamnatin tarayya ta bakin ministan harkokin waje Yusuf Tuggar, yace gwamnatin Najeriya ce ta bawa Amurka izinin kai harin bayan musayar bayanan sirri da manufar yaƙar rashin tsaro.
Nan gaba ma akwai ƙarin hare haren da Amurka za ta kaiwa yan ta’adda, inji ministan.
Amma wasu daga cikin al’umma na tambayar cewa , mai yasa Amurka ta zaɓi kai hari zuwa Sokoto, saɓanin Borno, wadda tayi kaurin suna a wajen tattara kungiyoyin ƴan ta’adda na Boko Haram, ISWAP da sauran su.
Har ila yau akwai masu cewa shin ƴan ta’adda nawa harin na Amurka ya kashe a Sokoto.
Durumin iya
Daily News 24

