Ɗan Takarar ADP, Bashir Aliyu Hausawa, Ya Ƙaddamar da Feshin Maganin Sauro a Ɗorayi
Ɗan takarar jam’iyyar Action Democratic Party (ADP) mai alamar littafi a zaɓen Majalisar Dokokin Jihar Kano, mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Gwale, Hon. Dr. Bashir Aliyu Hausawa, ya ƙaddamar da shirin feshin maganin sauro a unguwannin Ɗorayi Ƙarama da Ɗorayi Babba, domin inganta lafiyar al’umma da kare mazauna yankunan daga cututtukan da sauro ke yaɗawa.
Wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin da yake yi na yaƙi da cutar zazzabin cizon sauro da inganta lafiyar mazauna waɗannan yankuna.
An gudanar da aikin feshin maganin sauro ne da nufin rage yawaitar sauro da kuma rage haɗarin kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro tsakanin al’umma.
Wannan mataki ya nuna muhimmancin rigakafin cututtuka da haɗin gwiwar al’umma wajen kare lafiyar jama’a da samar da muhalli mai tsafta da aminci ga mazauna Ƙaramar Hukumar Gwale.
