Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) ya Yabi Ƙungiyar NUJ ta Kano a lokacin Kaddamar da Ofishin Sashen Jaridun Yanar Gizo ta farko a jahar Kano.
Shugaban Ƙungiyar ‘Yanjaridu ta Najeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, ya yaba wa ƙungiyar NUJ reshen Jahar Kano bisa sababbin abubuwan da su ke ƙirƙira da jagorancin haɗin guiwa da kuma tsare-tsaren da suke na haɗa kan ƴaƴanta(yanjarida).

Kwamared Yahaya ya yi wannan yabo ne yayin liyafar dare da bayar da lambar yabo kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya a lokacin rufe makon ‘yan jarida na shekarar 2025 da reshen NUJ ta Kano ta shirya, wanda aka gudanar a ranar Asabar a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Kano. Ya bayyana cewa ƙungiyar Kano na daga cikin rassan da koyaushe yake alfahari da su, tare da yabawa shugabanni a matakai daban-daban bisa jajircewa da aiki tare.
Shugaban na NUJ ya kuma nuna godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ƙaunarsa da aikin jarida da kuma saka jari da yake yi a fannin aikin jarida. A cewarsa, goyon bayan gwamnan ya taimaka matuƙa wajen ƙarfafa aikin jarida a jihar.
Yayin da yake kiran ‘yanjarida da su rungumi ƙwarewa da alhakin aiki yayin shirin shiga shekarar 2026, Kwamared Yahaya ya bukaci mambobi da su zama jakadu na kwarai ga aikin jarida ta hanyar tsara sahihin jadawalin aiki da kare martabar aikin jarida a Najeriya.
Ya ƙara bayyana cewa shugabancin ƙasa na NUJ yana ci gaba da ƙoƙari wajen kawo sababbin tsare-tsare da suka haɗa da inganta albashi ga ‘yan jarida da ke aiki a kafafen yaɗa labarai na gwamnatin tarayya. Ya ce ana ci gaba da tattaunawa da Ministan Yaɗa Labarai, tare da nuna kyakkyawan fatan cewa idan an aiwatar da wannan mataki a matakin tarayya, ƙungiyar za ta matsa lamba a aiwatar da shi a jihohi 36 na ƙasar.
Kwamared Yahaya ya kuma bayyana shirin ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya ga ‘yan jarida, da nufin rage nauyin kuɗin magani daga aljihunsu, rage mace-macen mata masu juna biyu, da kuma tallafa wa shirin samar da inshorar lafiya ga kowa da kowa.
Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Kano, ya jaddada kudurin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da kula da walwala da ci gaban aikin ‘yan jarida. Ya bayyana wasu sauye-sauyen da ma’aikatar ta kawo ciki har da shirye-shiryen habaka ƙwarewar yanjarida, tsara dokar yaɗa bayanai ta jihar, haɗa ‘yanjarida na kafafen yada labarai na kowanne bangare.
Tun da farko, Shugaban NUJ na Jihar Kano, Kwamared Sulaiman Dederi, ya ce makon ‘yan jarida na shekarar 2025 an tsara shi ne don ƙarfafa haɗin kai da haɗin guiwa tsakanin mambobi. Ya bayyana cewa ayyukan da aka gudanar sun haɗa da addu’o’i, wasan sada zumunta, horo, da ziyartar mambobin da ke fama da rashin lafiya da iyalan waɗanda suka rasu.
An kammala taron ne da bayar da lambobin yabo ga Kwamishinan Yaɗa Labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya; tsohon Shugaban Ƙungiyar Editoci ta Ƙasa, Baba Halilu Dantiye; da Darakta Janar na Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa ga Gwamnan Jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa. Har ila yau, an kaddamar da ofishin yanjarida na yanar Gizo-gizo .