eMagazine Media Channel Featured NUT TA BIYA WA WASU MALAMAI KUƊIN SADAKIN AURE A NASSARAWA LG
Featured

NUT TA BIYA WA WASU MALAMAI KUƊIN SADAKIN AURE A NASSARAWA LG

IMG 20260116 WA0026

IMG 20260116 WA0026

ƘUNGIYAR NUT RESHEN KARAMAR HUKUMAR NASSARAWA DA KE KANO TA BIYA WA WASU MA’AURATA KUƊIN SADAKIN AURENSU.

Ƙungiyar malamai ta NUT dake karamar hukumar Nassarawa ta ɗauki nauyin biya wa wasu malaman makaranta da su ka daidaita kansu domin yin aure tare a ranar Juma’a 15/1/2026 kamar yadda Kungiyar ta NUT ta saba yi a kullum.

Shugaban ƙungiyar Comrade Nura Lawal ya bayyana wa wakilin E-Magazine Media Channel cewa, ” Kungiyar NUT ta biya wannan kuɗin sadakin ne ga Malam Ali Muhd , wanda yake malami ne a makarantar Gwagwarwa Special Primary School. Malam Ali ya samu amincewar wata malama dake karamar hukumar Nassarawa wadda su ka fahimci juna da ya kai su ga yin Aure tare.”

Nura ya ce, “wannan ba shi ne farau ba dan an yi irin wannan biyan kudin sama da sau goma a cikin shekaru biyu.” Comrade Nura ya yi wa ango da amarya fatan alkhairi.

A nasa jawabin ango Malam Ali Muhd ya ce , ya ji daɗin wannan tallafi da aka bashi na biya masa sadakin auren Malama.

Angon ya yi godiya ga kungiyar NUT reshen karamar hukumar Nassarawa bisa taimakonsa da aka yi na biya masa sadakin aure. Ali ya jaddada goyon bayansa ga ƙungiyar tare da kira ga malaman makaranta da suma su yi biyayya da godiya ga ƙungiyar ta NUT.

Baba Comrade, E-magazine.

15/1/2026

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version