eMagazine Media Channel Uncategorized NUT TA BA WA MALAM HAFIZU IBRAHIM UMAR TALLAFIN KUƊIN MAGANI
Uncategorized

NUT TA BA WA MALAM HAFIZU IBRAHIM UMAR TALLAFIN KUƊIN MAGANI

IMG 20260804 WA0014

IMG 20260804 WA0014

NUT TA BA WA MALAM HAFIZU IBRAHIM UMAR TALLAFIN KUƊIN MAGANI

Kungiyar NUT ta jahar Kano bisa jagorancin Comrade Baffa Ibrahim Garko ta ba wa Malam Hafizu Ibrahim Umar da ke malami a makarantar Tamburawa Central Primary School, Dawakin Kudu tallafin Naira dubu ɗari (100,000) ta hannun Comrade Aminu Hassan Adamu, 2nd Vice Chairman.

Comrade Aminu Hassan Adamu wanda ya wakilci shugaban ƙungiyar NUT na jahar Kano, ya ce an ba wa Malam Hafizu Ibrahim Umar ne wannan tallafi na kuɗi ne, saboda hatsarin da ya rutsa da shi wanda ya jawo rasa ƙafarsa ɗaya.

Adamu ya yi addu’ar Allah ya ba wa Malam Hafizu Ibrahim Umar lafiya tare da fatan Allah ya sa wannan jarabawar da ta same shi ta zama kaffara a gare shi .

Malam Hafizu Ibrahim Umar ya yi jawabin godiya ga dukkanin shugabannin NUT na jahar Kano dana ƙaramar hukumar Dawakin Kudu bisa wannan kula wa da akai da shi akan wannan iftila’i da ya same shi.

A nasa jawabin shugaban ƙungiyar malaman makaranta reshen ƙaramar hukumar Dawakin Kudu ya yi jawabin godiya a madadin dukkannin malaman makaranta na ƙaramar hukumar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version