NUT DEPUTY NA GWALE YA BA WA MALAMAN MAKARANTA SU KIMANIN 48 TALLAFIN AZUMIN WATAN RAMADAN
A ranar Alhamis 5 ga watan Maris shekara ta 2026 mataimakin shugaban kungiyar Malaman makaranta na Gwale, Comrade Yusuf Sadi ya ba wa wasu malaman makaranta su kimanin 48 kuɗaɗen da za su yi amfani da su domin a matsayin tallafin Ramadan.
Kwamared Sadi, ya yi karin haske a inda ya shaida wa malaman cewa, insha Allahu daga wannan lokaci zai ci gaba da tallafa wa malaman makaranta musamman a dukkanin watan Ramadan fiye da irin wanda aka bayar a wannan lokaci. Ya kuma nemi malaman makaranta da su taya shugaban ƙungiyar NUT na jahar Kano Comrade Baffa Ibrahim Garko da ADDU’O’I na musamman akan kokarin da ya ke yi na ganin an daidaita albashin malaman makaranta na Primary.
A nasa jawabin jagoran matasa na Gwale ya ce, abun da ya kamata dama a ce duk wani shugaba kuma me iko yana yi. Ya ce tabbas Malam Yusuf Sadi Mutum ne mai son yin taimako da kuma kishin malaman makaranta. Wanda hakan ne ma ya sa su ka yi ƙoƙari wajen ganin an shigo da shi cikin kungiyar ta malaman makaranta.
Comrade A’isha Sani ta yi godiya ta musamman a madadin malamai mata bisa wannan tallafi na kuɗi da Deputy na NUT Gwale ya ba su.
A nasa jawabin Dr Nazifi, HOU JSS, Gwale LGEA wanda ya wakilci shugaban hukumar ta ilimin Gwale ya ce, LGEA ta yi farin ciki sosai da ta ga wannan gagarumin aikin ALKHAIRI da NUT Deputy chairman ya yi , wanda abun a yaba ne. Nazifi ya yi godiya sosai a madadin shugaban Gwale LGEA.
Wasu daga cikin wadanda su ka samu wannan tallafi mun tattauna da su , a inda su ka nuna farin cikinsu tare da addu’ar fatan alkhairi ga Comrade Yusuf Sadi.
Baba Comrade, E-magazine
Daga Gwale
5/3/2025

