eMagazine Media Channel Condolences NUJ Online Media Chapel na Alhinin Rasuwar yanmajalisun jahar Kano masu wakiltar Ungogo da Kano Municipal !
Condolences

NUJ Online Media Chapel na Alhinin Rasuwar yanmajalisun jahar Kano masu wakiltar Ungogo da Kano Municipal !

IMG 20251224 WA0023

NUJ Online Media Chapel na Alhinin Rasuwar yanmajalisun jahar Kano masu wakiltar Ungogo da Kano Municipal !

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Online Media Chapel na Jihar Kano, ta bayyana matuƙar alhini da jimami kan rasuwar fitattun ‘yan majalisar dokokin jihar Kano guda biyu — Hon. Aminu Sa’ad Ungogo da Hon. Sarki Aliyu Daneji — waɗanda suka wakilci mazabun Ungogo da Kano Municipal.

A cikin wata sanarwar ta’aziya, kungiyar ta bayyana rasuwar ‘yan majalisun a matsayin babban rashi mai raɗaɗi .

Hakika an yi rashin jajirtattun shugabanni masu hangen nesa da kuma ƙwarewa a cikin harkokin shugabanci da wakilci.

1766593711796

Shugaban ƙungiyar Comrade Abubakar Abdulƙadir Ɗangambo, ya miƙa sakon ta’aziya ga iyalan mamatan da Megirma Gwamnan Jahar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano Rt. Hon. Jibrin Isma’il Falgore, da dukkan ‘yan majalisar da al’ummar Kano baki ɗaya.

A cikin sanarwar da ya rattaba wa hannu, Comrade Ɗangambo ya bayyana cewa, wannan rashi ba wai na iyalansu kadai ba ne, illa rashi ne babba da ya shafi jihar Kano da ƙasa gaba ɗaya. Ya ce rashinsu da aka yi a majalisar ya haifar da gibi mai wahalar cikewa, la’akari da jajircewarsu da ƙwarewa a aikin gwamnati.

A madadin membobin NUJ Online Media Chapel na Kano, Shugaban Chapel ɗin ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta musu, Ya jikansu, Ya kuma ba iyalansu haƙuri da ƙarfin zuciya don jure wannan babban rashi.

A tuna cewa Hon. Aminu Sa’ad Ungogo da Hon. Sarki Aliyu Daneji sun riga mu gidan gaskiya ne a ranar Laraba bayan fama da rashin lafiya .

Comrade Abubakar Abdulƙadir Ɗangambo

Shugaban, NUJ Online Media Chapel, Kano State

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version