eMagazine Media Channel Education MURTALA MEGARANTI YA KAMA AIKI A MAKARNTAR GSS KAWAJI 
Education

MURTALA MEGARANTI YA KAMA AIKI A MAKARNTAR GSS KAWAJI 

IMG 20260211 115218 032

IMG 20260211 115218 032

MURTALA MEGARANTI YA KAMA AIKI A MAKARNTAR GSS KAWAJI

A ranar Laraba 11/2/2026 sabon Principal da aka kai makarantar GSS Kawaji, Comrade Murtala Megaranti ya kama aiki nan take . A inda su ka yi HAND OVER da mukaddashin tsohon principal kuma retired Malam Bala.

An yi wannan hand over ne a cikin makarantar ta Kawaji a gaban Zonal Director na Nassarawa ZED da kuma wakilai na shugabancin kungiyar malaman makaranta ta Nigeria (NUT) da kuma sauran malaman makaranta na GISS Dakata dana GSS Kawaji da kuma Fagacin Bichi Alhaji Haruna Megaranti.

Zonal Director na Nassarawa Alhaji Bello Dankade ya yi jawabai masu yawa a inda ya ba wa malamai da sabon Shugaban makarantar ta GSS Kawaji Shawara akan a yi aiki tare , a kuma zauna lafiya. Dankade ya ce , hakika Murtala Megaranti mutumin kirki ne kuma me kishin son ci gaban ilimi . Wanda hakan ne ma ya sa aka bashi wannan makaranta ta Kawaji . Saboda kokarinsa.

Dankade ya yi kira ga kungiyar PTA da SBMC da su mara wa sabon Principal baya domin ciyar da martabar makarantar da ma ilimi baki daya. Haka zalika ya ce wa sauran malaman su ma da su taimakawa sabon shugaban makarantar.

Alhaji Haruna Megaranti Fagacin Bichi ya ce , Murtala Megaranti Dan’uwansa ne na jini kuma a saninsa mutum ne mai tsari da Policy kuma mai son ganin an yi gaskiya a kowanne al’amari.

A nasa jawabin Shugaban ƙungiyar malaman makaranta na Nassarawa (NUT) Comrade Nura Lawal Hassan ya ce, Kungiyar NUT aka ba wa shugabancin wannan makaranta, domin Murtala Megaranti shi ne NUT Secretary na Nassarawa Branch. Dan haka NUT ba za ta ba wa malamai kunya ba. Lawal ya ce, NUT kullum a shirye ta ke wajan hidimtawa malaman makaranta na Primary dana Secondary.

A karshe ya ce , ya kamata malamai su san cewa, NUT ce kadai kungiyar malaman makaranta na Primary dana Secondary. Kuma ya kamata malamai su daina yawan gulma da hada rigima a dukkanin makarantu.

Comrade Salisu Al Hassan wanda shi ne sakataren PTA na jahar Kano kuma Treasurer na NUT ya ce, PTA a shirye ta ke ita ma wajan ganin ta mara wa sabon Principal na GSS Kawaji baya da bashi duk wani taimakon da ake bukata. Al Hassan ya kuma yi wa malaman makaranta nasiha akan yin aiki cikin gaskiya da amana

A nasa jawabin sabon shugaban makarantar ta GSS Kawaji Comrade Murtala Megaranti ya yi jawabin godiya ga dukkanin malaman makaranta da suka yi masa rakiya zuwa sabon wajan aikin nasa.

Baba Comrade, E-magazine

11/2/2026

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version