Kungiyar NYA Ta Gudanar da taron Matasan jahar Kano tare da Sake Jaddada Kudurin taimakawa ci gaban Jahar Kano.
Majalisar Matasan Arewa (NYA) ta sake tabbatar da aniyarta na ƙarfafa wa matasan Jahar Kano da ma sauran sassan ƙasa guiwa domin su ɗauki ragamar makomarsu da zama masu dogaro da kai.

Sakataren Ƙasa na ƙungiyar, Dr. Hafiz Garba, ya bayyana haka a wajen jawabin maraba da ya yi a taron Matasan dukkanin Kano na kwana ɗaya da aka gudanar a ranar Litinin 5/1/2025 a makarantar Northwest University, Kano.
A cewarsa, ci gaba mai ɗorewa ba zai samu ba sai matasa sun daina yin korafi, Sannan su sama wa kansu mafita me amfani gan magance ƙalubalen al’umma.
Sakataren ya ƙara da cewa, “Ya ku matasan Kano, ku samar da haɗin kai da zai haifar da ci gaba.”
Taken taron shi ne “Kafa Manufa Don Ci Gaban Jihar Kano.”
A jawabin sa a taron, bako mai magana kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ƙarfafi matasa da su tashi tsaye su yi aiki tukuru wajen gina rayuwa mai ma’ana dan ci gaban kansu dana al’umma.
Kwamishinan ya jaddada cewa rayuwa mai kyau tana buƙatar gaskiya, himma, ƙuduri da ƙwazo, tare da ba da shawarwari ga matasa su kasance masu haƙuri da tsara tsare-tsare wajen cimma burinsu na gaba.
A wannan taro an samu halartar wakilai daga hukumomin tsaro ciki har da Department of State Services (DSS), Ƴan Sanda na Najeriya, da hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA). Haka kuma an samu mahalarta daga manyan makarantu, shugabannin ƙungiyoyin ɗalibai, kungiyoyin matasa da mata, da masu aikin jarida.
Daya daga cikin manyan abubuwan da suka yi fice a taron shi ne bada Lambobin yabo na Girmamawa ga Gwamnan Jahar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya,da kuma wasu fitattun ’yan kasuwa da masu gudanarwa, don nuna godiyar irin gudummawar da suka bayar wajen ci gaban matasa da shugabanci.