A ranar Alhamis 4/12/2025 Qungiyar malaman makaranta ta NUT tare da haɗin guiwa da kungiyar Hedimastoci ta AOPSHON dake Karamar hukumar Tudunwada sun kai ziyarar dubiyar rashin lafiya ga daya daga cikin Head Teachers na karamar hukumar Tudun malam TALLE SA’IDU (Shobo)

Bisa rashin lafiyar daya kwashe watanni a kwance.
Shugaban ƙungiyar ta NUT Comrade Haruna Abdu ya ce, sun kai wa malam Talle tallafin kuɗaɗen shan magani tare da yi masa addu’ar neman sauki a wajan Allah SWT .
Comrade ya yi kira ga sauran malamai da yan’uwa da abokan arziki da su taimaka wa malam Talle da addu’a tare da sauran masu neman taimako irinsa.