Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bukaci Majalisar Dokokin Amurka da ta cire sunan tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, daga kudirin dokar da ake shirin gabatarwa kan zargin tauye ‘yancin addini a Najeriya.
Gwarzo ya bayyana zargin da ake yiwa Kwankwaso a matsayin mara tushe,Kuma bai dace da tarihinsa na aiki ba. Yace a tsawon fiye da shekaru talatin da Kwankwaso ya shafe yana rike da manyan mukaman siyasa—ciki har da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Gwamna sau biyu, Ministan Tsaro, Sanata da dan takarar shugaban kasa—ba a taba tuhumar shi ko gurfanar da shi kan tsattsauran ra’ayin addini ko take hakkin dan Adam ba.
Ta cikin wata Takarda da
Sakataren Yada Labarai na Mataimakin Gwamna Ibrahim Garba Shuaibu ya Rabawa Manema labarai,
Mataimakin gwamnan ya jaddada cewa Kwankwaso ya kasance mai adawa da tashin hankali, tsattsauran ra’ayi da ta’addanci, tare da kyakkyawar mu’amala da shugabannin Kirista da kananan kabilu a lokacin mulkinsa. Ya kawo misalin hadakar takarar shugaban kasa ta 2023 da Bishop Isaac Idahosa a matsayin hujja ta goyon bayansa ga hadin kan addinai.
Gwarzo ya bukaci ‘yan majalisar Amurka da su yi watsi da shawarar gaba ɗaya tare da cire sunan Kwankwaso daga kudirin dokar, yana zargin cewa an saka sunansa ne saboda son zuciya ko rikicin siyasa.

