eMagazine Media Channel Education Gwamnatin Kano Ta Miƙa Makarantar Rano Ga Kwamitin Kafa Federal Polytechnic
Education

Gwamnatin Kano Ta Miƙa Makarantar Rano Ga Kwamitin Kafa Federal Polytechnic

IMG 20260330 WA0003(1)

IMG 20260330 WA0003(1)

Gwamnatin Kano Ta Miƙa Makarantar Rano Ga Kwamitin Kafa Federal Polytechnic

Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa Makarantar Fasahar Karkara da Bunƙasa Harkokin Kasuwanci (School of Rural Technology and Entrepreneurship Development), Rano, ga Kwamitin Gudanarwa da ke kula da kafa Federal Polytechnic ta Rano.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Lahadi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin bikin miƙa makarantar, inda ya gana da mambobin Kwamitin Gudanarwar tare da duba wasu gine-gine da kayan aiki da aka ware domin bunƙasa sabuwar Federal Polytechnic ɗin.

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta samar da dukkanin goyon bayan da ya dace domin tabbatar da nasarar kafa makarantar da kuma fara karatunta cikin gaggawa.

Ya jaddada muhimmancin ilimin fasaha da koyon sana’o’i, yana mai cewa hakan na da matuƙar muhimmanci wajen shirya matasa domin samun aikin yi, bunƙasa kasuwanci da kuma dogaro da kai.

Gwamna Yusuf ya kuma bayyana cewa gwamnatin Kano za ta inganta gine-gine da sauran abubuwan more rayuwa, tare da kyautata yanayin koyo da koyarwa a sabon wurin makarantar da ke Ƙaramar Hukumar Sumaila, domin tabbatar da ingantaccen ilimi.

Gwamnan ya nuna godiyarsa ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Sanata Kawu Sumaila, da Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, bisa jajircewarsu da ƙoƙarinsu wajen ganin an tabbatar da kafa Federal Polytechnic ta Rano.

Haka kuma, ya yabawa mambobin Kwamitin Gudanarwar bisa ci gaba da ƙoƙarinsu da sadaukarwar da suke nunawa, wanda ya ce ya taimaka matuƙa wajen kusantar da aikin zuwa matakin kammalawa.

A nasa jawabin, Sanata Kawu Sumaila da Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum sun gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da kafa Polytechnic ɗin, tare da nuna godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda samar da goyon baya da yanayin da ya dace domin ganin an tabbatar da aikin.

Sun bayyana fatansu na cewa sabuwar makarantar za ta ƙara faɗaɗa damar samun ilimin fasaha, inganta koyon sana’o’i, tare da samar da sabbin damammaki ga matasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version