Gida Gida Network Strategies Campaign for AKY ta bayyana cikakken goyon baya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf
Ƙungiyar Gida Gida Network Strategies Campaign ta bayyana cikakken aniyarta na bai wa maigirma Gwamnan Jihar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf, goyon baya mara ƙaƙƙautawa, tare da yin alƙawarin yin aiki tare da gwamnatinsa domin cimma ci gaba mai dorewa a faɗin jihar.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana muhimman fannoni da za ta mayar da hankali a kai domin ƙarfafa shugabanci da inganta rayuwar al’umma. Waɗannan sun haɗa da tallafa wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati, wayar da kan jama’a kan muhimmancin haɗin kai da zaman lafiya, da kuma nuna tasirin alherin ayyukan gwamnati.
Har ila yau, ƙungiyar ta jaddada ƙudirinta na ƙarfafa wa matasa da mata, tare da ƙarfafa musu guiwa wajan taka rawa a harkokin ci gaban jihar.
Bugu da ƙari, ƙungiyar ta bayyana cewa goyon bayanta bai tsaya ga lokacin zaɓe kawai ba, inda ta sake tabbatar da aniyarta ta tsayawa tare da wannan gwamnati tsawon wa’adinta domin tabbatar da cimma manufofinta, musamman wajen inganta rayuwar al’ummar Jihar Kano.
A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga al’umma da su ba sabuwar gwamnati haɗin kai domin samar da zaman lafiya, ci gaba da wadata a faɗin jihar.
Sa hannu:
Babban Sakataren Gida Gida Network Strategies Campaign, Hon. Umar Yushau Rurum.
