eMagazine Media Channel LABARAI Ghana: An nada Farfesa Bashir Aliyu Umar jagoran Majalisar aiwatar da harkokin bankin da babu kuɗin ruwa na Kasar
LABARAI

Ghana: An nada Farfesa Bashir Aliyu Umar jagoran Majalisar aiwatar da harkokin bankin da babu kuɗin ruwa na Kasar

FB IMG 1787226592977 768x512

FB IMG 1787226592977 768x512

Ghana: An nada Farfesa Bashir Aliyu Umar jagoran Majalisar aiwatar da harkokin bankin da babu kuɗin ruwa na Kasar

Madogara: Independent

Gwamnan Babban Bankin Johnson Pandit Asiama ya ƙaddamar da ƴan majalisar a ƙarƙashin jagoranci Umar lokacin wani ƙwarya ƙwaryar bikin da aka yi a birnin Accra.

A Yayin kaddamarwar, Asiama ya ce wannan bangare na harkokin bankin da babu kudin ruwa na ci gaba da samun karɓuwa a tsakanain al’umma, saboda haka ya na da muhimmanci a inganta shi da kuma kare maradun masu amfani da shi.

Gwamnan ya ce nasarar wannan bangaren ba zai tsaya ne a kan yawan sabbin hanyoyin da za’a gabatar na hada hadar bankin da babu ruwa a cikin sa ba, sai dai ingancin su da kuma karɓuwar su a wurin jama’a.

Shugaban Bankin ya buƙaci ƴan majalisar bada shawarar da su yi aikin su ta hanyar amfani da ƙwarewar su da kuma ficen da suka yi ba tare da katsalandan daga wani wuri ba, domin tabbatar da sahihancin bangaren hada hadar kudaɗe da nagartar sa domin biyan buƙatar jama’a.


 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version