Hukumar Civil Defence ta Jihar Kano ta sauke shugabar ofishinta na Karamar Hukumar Fagge, SC Amina Musa Kolawole, tare da maye gurbinta da CSC Bashir Isa Abubakar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin Hukumar Civil Defence ta Jihar Kano, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar da aka rabawa manema Labarai a ranar Juma’a 9/1/2026
Sanarwar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan wani lamari da ya haifar da mutuwar wani matashi mai suna Halifa Abdullahi Fagge.
Tun da farko, Babban Kwamandan Hukumar Civil Defence ta Jihar Kano, Mohammad Hassan Agalama, ya janye dukkan jami’an da ke bakin aiki a lokacin da lamarin ya faru a ofishin hukumar da ke Karamar Hukumar Fagge.
Haka kuma, hukumar ta mika jami’an ga Rundunar ’Yan Sandan jihar Kano domin ci gaba da gudanar da bincike.
A karshe, Hukumar Civil Defence ta Jihar Kano ta bai wa al’ummar jihar tabbacin ci gaba da kare hakkin jama’a da tabbatar da adalci a kowane lokaci.
Source: Mikiya

